Ana zargin Amal da yun?urin ba da cin hancin naira dubu 250 ga wani ?an sanda mai suna ASP Salisu Bujama da ke rundunar ?ansandan, shiyya ta ?aya da ke Kano.
A cewar mai gabatar da ?arar, Amal na yun?urin bayar da cin hancin ne domin hana binciken ?an sanda kan zargin saurayinta da almundahanar ku?i.
Lamarin ya bayyana ne lokacin da wani Yusuf Adamu ta hannun lauyansa ya shigar da ?orafi ga mataimakin babban spetan ?ansanda Umar Mohammad Sanda, inda yake zargin saurayin jarumar da yin sama da fa?i da ku?in da ya kai naira miliyan 40 da sunan kasuwanci.
?orafin da aka shigar ya sa ?ansanda gudanar da bincike wanda ya gano cewa saurayin jarumar ya tura mata naira miliyan 13 ta asusun bankinta.
Acewar kakakin rundunar ?ansanda shiyya ta ?aya, CSP Bashir Muhammed, an gayyaci ?ar fim ?in domin amsa tambayoyi daga bisani kuma aka bayar da belinta sai dai an hana ta fita daga wata mota da ake zargin saurayin nata ne ya siya.
Jarumar ta tabbatar cewa ku?in da ke cikin asusunta mallakin saurayinta ne duk da ta yi i?irarin cewa naira miliyan takwas kawai ya tura mata.
Bayan da aka ba ta beli ne kuma ta garzaya babbar kotu a Kano domin neman a dakatar da ?ansanda daga binciken da suke a kanta. Kotun ta hana ci gaba da binciken da ?ansanda ke yi kan jarumar, abin da ya bai wa Amal dama ta yun?urin ba da toshiyar baki ga ?ansandan da ke binciken ASP Salisu Bujama.
Jami’in ya yi watsi da cin hancin inda kuma ya kamata ta tare da shaidar zargin ba da cin hancin abin da ya sa aka gurfanar da ita gaban kotun majistre ranar Laraba.
Laifin da ake zargin jarumar ta aikata ya sa?a sashe na 118 na dokar penal code wadda ta haramta bai wa jami’in ?ansanda cin hanci.

