Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar A ranar Alhamis, Sheikh Abduljabbar Nasiru-Kabara, ya fara gabatar da nasa hujjojin gaban kotu a shari’ar dake gudana tsakaninsa da gwamnatin jihar Kano.
AbdulJabbar ya gabatar da litattafai 27, ciki akwai Almuhadisu Alfasil Banul Rawawil Wali, Sunannun Darumi, Jamiu Ilmi, Tauhiful Afkar, Anannakatu Almukaddimatu Ibn Salah, Al Gaya, da sauransu.
A baya an ruwaito cewa an shigar da Malam AbdulJabbar kotu bisa zargin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) lamarin da ya sanya malamai yin mukabala dashi kafin daga bisani aka tura shi Kotu.
Gabanin fara jawabinsa a kotu, AbdulJabbar ya rantse da Alqur’ani mai girma cewa bai zagi Annabi ba, Yace: “Kawai ina kare mutuncin Annabi Muhammad (SAW) ne bisa kalaman da akayi akansa a cikin Hadisi.” “Abinda na gani cikin Hadisi na fassara. Ba sharhin kaina bane.” “A wa’azuzzuka na, ban yi batanci wa Annabi ba kan aurensa da Nana Safiya.”
Lauyan gwamnati, Suraj Sa’eda SAN ya bayyanawa kotu cewa AbdulJabbar ya yi kalaman batanci wa Annabi kan aurensa da Nana Safiyya a Jautul Fara a sashe na 93 (40) da hadisi da 1,365 da 1,428.
Alkalin kotun, Malam Ibrahim Sarki-Yola, ya bukaci AbdulJabbar ya baiwa lauyan gwamnati kwafin litattafan. Ya dage karar zuwa ranar 17 ga Marus don cigaba da zaman.

