Shugaban Kamfanin Atar Communication masu gidajen Talabijin da Rediyo na Liberty da Jaridun Muryar ‘Yanci da Voice Of Liberty Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan, ya taya al’ummar musulmi murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1443 bayan hijira.
Ramalan ya bayyana godiya ga Allah Ta’ala da ya raya mu muka shaidi wannan muhimmiyar shekara mai albarka ta musulunci, tare da fatan Allah ya sada mu da albarkatun dake cikin ta amin.
Shugaban Liberty Talabijin ya bukaci jama’a da su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa ?asa addu’a da fatan Allah ya kawo mana karshen matsalolin dake addabar ?asar nan.
Shugaban ya kuma mika godiyar shi ga dimbin masoya da ke bibiyar kafafen ‘yanci, inda ya sha alwashin kara inganta ayyukan kamfanin yadda zai dace da biyan bukatun al’umma.

