Kamfanin sufurin jirgin sama na Emirates mallakar Daular Larabawa wato United Arab Emirate (UAE) ya ce zai sake dakatar da zirga-zirga zuwa Najeriya daga ranar 13 ga Disamba.
Matakin kamfanin na zuwa ne bayan hukumar kula da sufurin jirgi ta Najeriya NCAA ta ta?aita wa kamfanin shiga Najeriya ta Abuja da Legas.
NCAA ta zargi hukumomin Daular Larabawa (UAE) da ?in bai wa Air Peace, kamfanin Najeriya ?aya tilo da ke shiga UAE, damar shiga birnin Dubai ta Sharjah.

