Dan takarar Shugabancin Jamiyyar PDP na jihar Kaduna Edward Pama Auta, ya bayyana aniyarsa na dawo da martabar Jamiyyar da ha?a kan daukacin yayan jamiyyar a matakai daban-daban idan ya samu nasarar lashe za?en Shugabancin Jamiyyar wanda zaa gudanar nan gaba kadan.
Edward Pama Auta, ya bayyana haka ne yayin da ya kaiwa tsohon Shugaban jamiyyar PDP na kasa Kuma tsohon Gwamnan jihar Kaduna Sanata Ahmed Mohammed Ma?arfi a gidansa dake Kaduna domin neman goyon bayansu inda yayi Alkawarin Farfado Da martabar Jamiyyar.
Auta, ya tabbatarwa tsohon Shugaban cewa idan ya samu damar zama shugaban jamiyyar PDP zai tabbatar da cewa ya kara ha?a kan yan jamiyyar da kuma dorawa akan irin gudummawar da tsohon Gwamnan ya tsaya wajen samar da zaman lafiya a fadin jihar Kaduna.
Yace jihar Kaduna ba zata mance da irin gudummawar da Makarfi ya kawo ba wajen samar da ayyukan ci gaba da samar da zaman lafiya wanda ba zaa ta?a mantawa da shi ba.
Na kawo maka wannan ziyarace domin neman goyon bayan ka da bayyana maka aniyata na yin takarar shugaban jamiyyar PDP na jihar Kaduna Wanda idan na samu nasara ba zan baka kunya ba wajen bun?asa cikin ci gaban jamiyyar a fa?in jihar baki ?aya inji shi.

