Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ‘Yan bindigar da suka sace daliban makarantar Bethel Baptist sun nemi karin wasu Miliyoyi bayan ana zargin sun karbi miliyan N100m tare da alkawarin sakin daliban dake hannunsu kashi-kashi, ?arayin sun sa?a alkawarinsu.
Yan bindigan sun karya alkawarin da suka yi ne ta hanyar turo da sabuwar bukata ta naira miliyan N50m kafin su sako ragowar ?alibai 83.
Wata majiya mai karfi ta shaidawa Vanguard cewa: “Bayan iyayen yaran sun tattara miliyan N100m sun mikawa yan bindigan domin a sako ‘ya’yansu, ?arayin sun turo da dalibai 28 tare da al?awarin sakin sauran kashi-kashi.”
“Amma a yanzun sun sake neman a basu ku?i miliyan N50m sannan su sako ragowar 83 dake hannunsu.”
“Yanzun iyayen sun cire tsammani kuma sun shiga halin ru?ani da jin wannan labarin saboda sun siyar da komai da suka mallaka sun ha?a miliyan N100 da aka baiwa yan bindigan.”
Saidai anashi ?angaren Shugaban yan Baptist reshen Kaduna, Ishaya Jangado, yace sam ba shi da labarin sabuwar bukatar, domin basu sake ji daga yan bindigan ba.

