Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar akalla mutum daya ya rasa rayuwarsa yayinda akayi awon gaba da mutum 33 yayinda yan bindiga suka kai hari karamar hukumar Kachia dake jihar Kaduna.
Yan bindigan sun kai wannan hari ne a dare cikin garin Kachia kuma sun jikkata mutane da dama, rahotanni sun bayyana cewar Hakimin garin Kachia, Idris Suleiman ya tabbatar da aukuwan wannan lamari yayinda jami’an tsaro da kwamishanan tsaron jihar, Samuel Aruwan, suka kai ziyara.
Yadda harin ya auku Suleiman ya ce yan bindigan sun dira cikin garin misalin karfe 9 na daren Alhamis kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi. Ya ce da farko sun kai farmaki gidan Burodi inda suka sace mutum biyar kuma suka kashe direban mai gidan Burodin.
Daga bisani suka shiga unguwar MotherCat kuma suka sace mutum 28, cikin har da mai juna biyi. Ya kara da cewa kafin suka fita daga cikin garin, sai da suka kwashe kayayyakin yan kasuwa.

