Wasu ‘Yan Bindiga da ba’a san ko su wanene ba ?auke da manyan makamai sun sace babban Paston Majami’ar
Pentecostal Fellowship dake jihar Kaduna Pastor Emmanuel Bako da matar sa Sandra.
‘Yan Bindigar sun tarke fasto Emmanuel da Matarsa Sandra a filin taro da adduoin musamman na Kirsimeti mai suna Albarka camp, Fadan Kagoma, kusa da Kafanchan karamar hukumar Jemaa.
Kakakin rundunaryan sandan Kaduna Mohammed Jalige ya tabbatar da wannan alamari, sannan ya kara da cewa ‘Yan Bindigar sun afka wa filin taron ne da wajen karfe 8:30 na dare, ranar Kirsimeti.
Bayan Pastor Emmanuel da matarsa Sandara, akwai wani mutum daya da ‘yan Bindigar suka arce da shi.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da aukuwar haka.
Ya ce jamian tsaro ne suka fatattaki ‘yan Bindigar sai dai Allah bai basu saan cimma musu ba har suka gudu.
Jihar Kaduna ta yi kaurin suna wajen hare-haren yan taadda da masu garkuwa da mutane.

