Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kashe mutane 3 a kananan hukumomin Giwa da Zangon Kataf a jiya Litinin.
Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa jamian tsaro sun bada rahoton harin da ?an taadda suka kai a kauyen Garawa, Doka da Unguwan Yaya duka a yankin Fatika a karamar hukumar Giwa inda suka kashe mutane 2 tare da sace wasu da yawa.
Kwamishinan tsaro da alamuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya shaida cewa ?an taaddan sun kai hari wurin shakatawa a kauyen Wawan Rafi a karamar hukumar Zangon Kataf inda suka kashe mutum daya tare da jikkata 3.
Ya kuma shaida cewa jamian tsaro sun samu bindiga kirar AK47 guda 2 tare da katan 43 na alburushi a wurin wasu mutane 2 da aka kama kuma.
Ya bayyana cewa Gwamna Nasir El-RufaI ya bayyana bakin cikinsa kan lamarin ya kuma yi addua ga mamatan tare da jajantawa iyalan mamatan kan abin da ya faru.

