Site icon Muryar 'Yanci

Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane Da Kona Buhunan Masara A Kasuwar Giwa

‘Yan bindiga da dama sun rasa rayukan su a yayin harin da suka kawo a yankin Galadimawa dake karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

An kashe ‘yan bindigan ne a yayin da suka kawo farmaki a kasuwar Galadimawa mai ci mako-mako a yammacin yau Laraba, inda ‘yan banga guda biyu da wasu mazauna garin su biyar suka rasa ransu.

Majiyarmu ta tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun dira kasuwar ne da misalin karfe hudu na yamma inda suka bude wuta kan ‘yan bangan, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar biyu daga cikinsu.

‘Yan bangan da suka mutu sune Yusuf Magaji Iyatawa da Dabo Bafillace.

A yayin gudun ceton rai kuma ‘yan bindigan sun kashe mazauna yankin su biyar da suka hada da, Danjuma Haladu, Shuaibu Isyaku, Isyaku Adamu, Shehu Dalhatu da Musa Haruna Kerawa.

Wani direban tirela mai suna Alhaji Yusuf Tumburku wanda ya gama lodin masara buhu 330 mallakar wani dan kasuwa mai suna Alhaji Hamza Unguwan Lalle Giwa, an kona motar da masaran. Tare kuma da kona wata karamar mota.

Saidai su ma ‘yan bindigan ba su ji da dadi ba, domin a yayin guduwa jami’an tsaro sun bi sahun su inda suka kashe da dama daga cikin su.

Tuni dai Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Elrufai ya tura da sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa ransu, inda kuma ya jinjinawa sojoji da ‘yan sandan sakamakon kashe ‘yan bindigan da suka yi.

Exit mobile version