An shawarci jama’ar Jihar Kaduna da su sanya sabon Gwamnan jihar Sanata Uba Sani cikin adduo’i domin samun nasara wajen ciyar da jihar Kaduna gaba.
?an Majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Unguwar Sanusi daga yankin ?aramar Hukumar Kaduna ta Kudu Honorabul Muhammad Auwal Yahaya wanda aka fi sani da Yaro Mai Kyau ya bukaci hakan a yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Kaduna.
?an Majalisar ya ?ara da cewar kiran ya zamo wajibi ta la’akari da irin gogewa da za?a??en gwamnan ya ke dashi ta fuskar cigaban ?asa, wanda kowa ya ga haka a zaman da ya yi a majalisar Dattawa kuma babu shakka Jihar Kaduna za ta samu kyakkyawan cigaba ?ar?ashin jagorancin Uba Sani.
Honorabul Auwalu Mai Kyau ya taya za?a??en gwamnan murnar shiga gidan Gwamnati, sannan ya yi addu’ar Allah ya shige mishi gaba wajen sauke nauyin jama’ar Jihar.

