Rahotanni dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu Jami’an ‘yan sanda masu murabus a jihar sun fito zanga-zangar lumana ga hukumar fansho dake Jihar sakamakon mawuyacin halin da suke ciki.
Tsofaffin ‘yan sanda sun yi tattaki zuwa hedkwatar rundunar ‘yan sanda da ke Kaduna domin mika kokensu Sun dade suna korafin yadda hukumar fansho ke nuna musu mugunta tare da rashin tausayi wurin rike musu kudi.
Daga karshe dai tsofaffin ‘Yan sandan da sun fita zanga-zangar lumana kan rike musu kudade da hukumar fansho ta jihar Kaduna ta yi a ranar Litinin domin nuna wa duniya irin halin da suke ciki.
Tsofaffin Jami’an sun yi tattaki har zuwa hedkwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna domin mika kokensu inda suka jaddada cewa ba su da ra’ayin abinda suka kwatanta da “hukumar kisa”.
An dauki tsawon wani lokaci, jami’an ‘yan sanda a kasar nan suna ta kushe hukumar fansho sakamakon zargin da suke yi wa Hukumar na musguna musu da cutar da su.

