Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamna Nasir El-Rufai na jihar ya ce wanda zai gaje shi zai rufe gidaje tare da ragargajesu domin habaka jihar fiye da yadda yayi a jihar a yanzu.
Ya ce wasu jama’a na kallonsa a mai rusau kuma sun kosa wa’adin mulkinsa ya kare, sai dai kash abin da basu sani ba shine shi sharar fage ya yi amma asalin mai rusau yanan nan tafe a 2023.
Gwamnan wanda ya sanar da hakan a wata tattaunawa da aka yi da shi a gidajen rediyo a ranar Alhamis, ya ce mazauna jihar yanzu suna jinjina masa a kan yadda mulkinsa ke gyara birane, amma tabbas wanda zai gaje ni sai yayi rusau da ragargazar gidaje fiye da ni.
Ya ce mulkinsa ya fi bada fifiko a habaka ababen more rayuwa fiye da rabawa jama’a kudi da sunan tallafi, “A lokacin da muka fara aiki kan gina makarantu, sun ce bamu samar da hanyoyi masu kyau ba. Yanzu muna aiki kan hanyoyi, amma suna cewa bamu tallafawa jama’a ba.
Idan rabawa jama’a kudi da dare shine abinda ake nufi da tallafawa jama’a, su cigaba da zaginmu. Talakawan da muke wa aiki ai suna godiya kan abinda muke yi.
Kun san zabe ya kusa kuma suna kallona a Mai Rusau. “A tunaninsu wanda zai zo bayana ba zai rushe komai ba. Amma rusau din da zai yi musu sai ya fi ni da izinin Allah,”
Daga ?arshe El Rufa’i yayi kira ga jama’a da su cigaba da goyon baya tare da yi wa mulkinsa addu’ar nasara.

