Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ?an takarar gwamnan jihar na jamiyyar APC, Sanata Uba Sani ya yi sulhu da abokin takarar sa da ya kada a zaben fidda gwani na jamiyyar APC Honarabul Sani Shaaban.
Idan ba a manta Sanata Uba Sani ya lallasa Shaaban da kuriu sama da 1000 in da Shaaban ya samu kuriu 16 kacal, sai dai kuma bayan zaben, Sha’aban ya bayyana cewa bai yarda da sakamakon zaben ba.
Hakan ya sa da yawa daga cikin masu yin sharhi akan zaben fidda gwanin ke ganin akwai sauran rina a kaba muddin Sanata Uba Sani bai yi sulhu da Sha’aban ba.
Hakan ya sa sanata Uba Sani ranar Litinin ya garzaya har gidan Sha’aban domin su yi sulhu don cigaban jamiyyar.
Uba ya ce Na tafi gidan Honarabul Sani Shaaban domin mu gana mu kuma tattauna da yin sulhu domin Jamiyyar mu da zaben dake tafe.
Shaaban gogagge ne a siyasa, kuma ina tabbatar muku cewa mun tattauna kuma yayi alkawarin lallai za mu yi aiki tare domin ganin jamiyyar ta yi nasara a zaben gwamna dake tafe.
Kowa ya san kwarewa da gogewar Honorabul Shaaban. Ya yi alkawarin zai hada hannu da ni kuma zai yi aiki tukuru wajen ganin jamaa sun karkata zuwa ga wannan tafiya don samun nasara a zabe mai zuwa.

