Site icon Muryar 'Yanci

Kaduna: Nazir Sanusi Ne Zabin Mu – Jama’ar Mazabar Kawo

An bayyana ?an takarar kujerar ?an Majalisar dokokin Jihar Kaduna mai waklitar Maza?ar Kawo karkashin jam’iyyar APCHonorabul Nazir Sanusi Abubakar a matsayin wanda ya zarce tsara kuma shi ne fata ga jama’ar yankin.

Al’ummar mazabar Kawo ne suka bayyana hakan a wata tattaunawa da suka yi da Wakilinmu da ya ziyarci yankin a ranar Juma’a.

Sun bayyana yankin nasu a matsayin wanda ya dade cikin koma baya sakamakon rashin samun kyakkyawan wakilci, amma cikin ikon Allah samun Nazir Sanusi cikin ‘yan takara ya sanya sun samu karsashi da ganin wanda zai kai yankin nasu ga nasara, kasancewar shi wanda ya yi kuma an gani a baya a mu?amin da ya ri?e na mataimakin shugaban ?aramar Hukumar Kaduna Ta Arewa.

A zantawar da ya yi da Wakilinmu ta wayar tarho Honorabul Naziru Sanusi Abubakar ya bayyana cewar damuwa da kishin jama’ar yankin nasu ne ya sanya shi fitowa takara domin bada gudunmawa na ciyar da yankin gaba.

Exit mobile version