Kungiyar Direbobin Tifa ta jihar ta bayyana cewar ba za ta rungume hannu tana kallon ana keta hakki da ‘yancin ‘ya’yan kungiyar ba ya zama dole su ?auki matakan da suka dace.
Sakataren kungiyar Direbobin Tifa na Jihar Kaduna Kwamared Musa Muhammad ?an Hajjah ne ya bayyana hakan a yayin ganawarsa da manema labarai a Kaduna.
Kwamared ?an Hajjah na tsokaci ne dangane da wani abin takaici da ya faru kwanakin baya tsakanin hukumar KASTELIA masu kula da ababen hawa a Jihar Kaduna da wani Direban tifa lamarin da ya kai har yaron Motar ya rasa ranshi.
Kungiyar ta bayyana wannan al’amari a matsayin abin takaici wanda ba za a lamunta tare da alkawarin yin dukkanin mai yiwuwa wajen kwato hakkin wanda aka zalunta.
Sakataren kungiyar Direbobin Tifan ya kuma bukaci ‘ya’yan kungiyar da su kasance masu bin doka da oda a duk inda suka tsinci kansu.
Sannan ya yi kira ga shugabannin hukumar KASTELIA da ?aukar mataki gami da horas da jami’an ta tsarin aiki yadda ya kamata.

