A ranar Litinin ne wani hasashen yanayi na BBC ya nuna cewa, mai yiwuwa ne ?asashen Afirka ta yamma ciki har da Najeriya su fuskanci ka?awar wata iska da ba a saba ganin irinta ba cikin kwana uku daga wannan Talatar har zuwa Alhamis.
Hasashen, wanda ita ma Hukumar kula da yanayi ta Najeriya Nimet ta tabbatar da shi na cewa, yanayin zai iya zuwa da mamakon ruwan sama, wanda ka iya haddasa ambaliyar ruwa da iska mai ?arfi.
Iskar wadda za ta taso daga ?asar Chadi, za ta ratsa ta arewacin Najeriya ta buga har zuwa ?asar Senegal.
Hasashen ya ce ruwan saman zai haifar da mummunan yanayi na ambaliya a yankunan na yammacin Afirka.
Shugaban hukumar kula da yanayi ta Najeriya, wato NIMET Farfesa Mansur Ba?o Matazu, ya shaida wa BBC cewa jiohin da ake hasashen za su fuskanci wannan ambaliya sun hada da Bauchi da Kano da Katsina da Zamfara da Kaduna da Kebbi da Sokoto da Neja.
Farfesa Ba?o ya ce a ranar Laraba jihar Zamfara da Kebbi da wani ?angare na Sokoto za su samu ruwan sama mai karfi da iska.
Sannan a ranar Alhamis ana saran lamarin zai shafi Jihar Taraba da Filato da ?angaren kudu wajen Enugu da kuma jihar Legas.
Farfesa Ba?o ya ce ana samun wannan yanayi ne sakamakon sauye-sauye na damuna wanda dama yawanci a farkon damina ruwan na zuwa babu karfi, sannan sannu a hankali zuwa karshen damina ruwa na karuwa.
Sannan ya ce ana cikin yanayi na iska mara karfi da ake kira ‘low pressure’ a Turance, to yanzu yanayin da ake ciki ana yawaita samun ha?uwar hadari da ruwa mai karfi.
Kuma yanayi a yanzu ya kai ma?ura har maki 23 a ma’aunin salshiyas a makonnin da suka wuce, sannan a yanzu da damina ke zuwa karshe yana kai wa maki 18.2 zuwa 17.2.
Kasashen Afirka da iskar zata shafa
Farfesa Ba?o ya ce baya ga Najeriya kusan duk ?asahen Afirka ta Yamma kama daga Togo da Burkina faso da Saliyo da Gambiya da Senegel duk za su fuskanci wannan yanayi.
Me ya kamata mutane su yi?
A tattaunawar da BBC ta yi da Farfesa Adamu Tanko, kwarare kan muhalli da sauyin yanayi a Jami’ar Bayero, ya ce akwai bukatar mutane su kasance suna sanya ido da rage wasu dabi’u.
Farfesa Tanko ya ce irin wannan yanayi ba abu ne da za a iya daukar wani mataki ko yin wani abu na daban ba, sai dai Farfesa ya ce ana iya yin wasu abubuwa kamar su kasance masu lura da yanayi kafin a fita.
Karin bayani
A kowacce shekara hukumomin kula yanayi na hasashen yadda damuna za ta kasance, da yawan ruwan da ake sa ran samu gami da yankunan da ake sa ran samun amabliya.
Su ma masana kan yi gargadi kan yiwuwar samun ambaliyar ruwa da jan hankalin mutane kan matakan kare muhallansu.
A bana ma dai akwai hasashen cewa a jihohi da dama na Najeriya za a iya fuskantar matsalar ambaliyar ruwa, sanadiyyar ruwan sama da kuma cika da batsewar koguna da tafkuna, inda tuni ma wasu yankunan suka fara fama da ambaliyar.
A Najeriya da ke da yawan al’umma sama da miliyan 186 a kullum ana fargabar karuwar al’ummarta da kuma rashin tsare-tsare masu inganci da za su kare unguwannin biranen.

