Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ‘Yan bindiga da ake zargin ‘yan fashin daji ne sun kashe a?alla mutum bakawai a yankunan Jihar Kaduna.
Kwamishinan Tsaro Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa ranar Asabar, inda ya ce jami’an tsaro ne suka shaida wa gwamnati faruwar lamarin.
A cewarsa, ‘yan fashi sun harbe mutum hu?u a wajen garin Tsohon Gayan da ke ?aramar Hukumar Chikun.
Kazalika, an kashe wasu mutum biyu da aka bayyana da suna Solomon Bamaiyi da Francis Moses a Kakau, sannan aka kashe wani da ba a bayyana sunansa ba a Kachia.
Ya ?ara da cewa wani mai suna Danjuma Alhaji mazaunin Tsohon Farakwai na ?aramar Hukumar Igabi ya rasa ransa a hannun ‘yan fashin a garin Galadima na ?aramar Hukumar Giwa.

