Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya sanar da sallamar masu rike da mukaman gwamnati mutum 99 da ya nada.
Gwamnan wanda ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Kaduna, ya ce wadanda aka sallama din sun hada da kashi 30 na masu rike da mukaman siyasa.
Ya ce jihar ta fara aiwatar da manufofinta na neman ‘yanci ta hanyar sallamar mutane 99 da aka nada a mukaman siyasa, amma har yanzu ba ta kori kowane ma’aikacin gwamnati ba.
Gwamnan ya bayyana cewa hukumomin da ke da nasaba da kananan hukumomi ne kawai suka kori maaikata, sun hadar da hukumar kula da ilimin makarantun framare SUBEB da Hukumar Kula da Kiwon Lafiya a matakin farko ta jihar.

