Site icon Muryar 'Yanci

Kaduna: Ba A Sauya Wa Jami’ar Jihar Suna Ba

Hukumar gudanarwar jami’ar gwamnatin jihar Kaduna KASU ta musanta labarin da ake yadawa cewa an sauya sunan jami’ar zuwa jami’ar Magajin Garin Zazzau.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Magatakardar jami’ar Samuel Mansho da Muryar ‘Yanci ta samu “kwafi”.

Sanarwar ta bukaci mutane da su yi watsi da wannan labari da ake ta yamadidi da shi.Tace idan ma har akwai wani bayani, duk za a ji su ne daga hukumar gudanarwar jami’ar nan gaba.

Tun bayan da labarin sauya sunan jami’ar ya fito zuwa sunan Magajin Gari Sambo, jama’a ke ta bayyana ra’ayoyin su akai, inda wasu ke ganin dacewar hakan, yayin da wasu ke ganin rashin dacewar.

Magajin gari Sambo dai ya fito ne daga zuriyar Sarki Musa Sarkin na farko a daular Fulani daga zuriyar Mallawa, zuriyar da Sarkin Zazzau na yanzu Ahmad Bamalli ya fito ciki, kuma gwamnan Jihar Kaduna El Rufa’i ke danganta kanshi da zuriyar.

Bayan wannan sanarwa da hukumar jami’ar ta fitar, za’a iya cewa an kulle dukkanin wani cece-kuce akai, abin jira dai a yanzu shine a ga me zai wakana a nan gaba.

Exit mobile version