Site icon Muryar 'Yanci

Kaduna: Atiku Ya Doke Tinubu A Akwatin Gidan Gwamna

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar ?an takarar shugaban kasa a inuwar People’s Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, ya lashe ?aya daga cikin rumfunan za?en da ke cikin gidan gwamnatin jihar Kaduna.

Atiku ya samu galaba kan babban abokin hamayyarsa na jam’iyya mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a rumfar zaben gidan gwamnatin mai lamba PU 013.

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa shugaban malaman zaben da suka yi a rumfar, Kalu kelechi Micheal, ya ratta?a hannu a kan takardar sakamakon za?en.

Sakamakon ya nuna cewa Atiku ya samu nasara da kuri’u 69, yayin da Peter Obi, ?an takarar shugaban kasa a inuwar Labour Party, ya zo na biyu da kuri’u 48.

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma ?an takarar APC mai mulkin Kaduna ya ta shi da kuri’u 40, sai kuma ?an takarar shugaban ?asa a inuwar NNPP, Rabiu Kwankwaso, wanda ya samu kuri’u 11.

Exit mobile version