Site icon Muryar 'Yanci

Kaduna: An Shawarci Jama’a Su Sanya Sabon Gwamna A Addu’a – Honorabul Salisu Isah

An shawarci jama’ar Jihar Kaduna da su sanya sabon Gwamnan jihar Sanata Uba Sani cikin adduo’i domin samun nasara wajen ciyar da jihar Kaduna gaba.

?an Majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Magajin Gari daga yankin ?aramar Hukumar Birnin Gwari Honorabul Salisu Isah ya bukaci hakan a yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Kaduna.

?an Majalisar ya ?ara da cewar kiran ya zamo wajibi ta la’akari da irin gogewa da za?a??en gwamnan ya ke dashi ta fuskar cigaban ?asa, wanda kowa ya ga haka a zaman da ya yi a majalisar Dattawa kuma babu shakka Jihar Kaduna za ta samu kyakkyawan cigaba ?ar?ashin jagorancin Uba Sani.

Honorabul Salisu Isah ya taya za?a??en gwamnan murnar shiga gidan Gwamnati, sannan ya yi addu’ar Allah ya shige mishi gaba wajen sauke nauyin jama’ar Jihar.

Exit mobile version