A karo na farko cikin sabuwar shekarar 2021, Shugaban Kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya fitar da sabon faifan bidiyo na sakon sautin murya tare da yin gargadi na musamman ga babban malamin addinin Islama, Sheikh Dakta Ahmad Gumi.
Jaridar Daily Nigerian ce ta sanar da hakan a wani takaitaccen sako da ta wallafa a shafinta a dandalin tuwita. Shekau ya gargadi Gumi akan alakanta kungiyar Boko Haram da Fulanin da ke yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
A ranar Lahadi ne Sheikh Gumi, fitaccen malamin addinin Islama, ya ziyarci wasu rugagen Fulani da suka yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa rugagen da Babban Malamin ya ziyarta sun kasance tamkar tarko wurin matafiya a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Amma, a faifan sautin murya mai tsawon mintuna 16 da ya saki ranar Talata, Shekau ya jaddada cewa kungiyarsa ba ta amfani da wasu ‘yan bindiga da ke garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja ko jihar Neja.
“Ba ma amfani da kowa wajen garkuwa da mutane domin neman kudin fansa. “Mun san akwai masu amfani da sunan kungiyar mu wajen garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, amma bama tare da duk irin wadannan kungiyoyi.
“Zamu yi aiki da duk mai son yin aiki tare da mu ko a Kaduna, Lagos, Benin, ko Amurka, amma mu kira muke yi zuwa ga Allah, ba dimokradiyya ko sabawa addini ba inji Shekau.
Yayin da ake tattaunawa da shi, Sheikh Gumi ya bayyana damuwarsa a kan yadda hanyar Kaduna zuwa Abuja ta zama abar tsoro saboda rashin tsaro tare da sanar da cewa jahilci ne yasa ake amfani da Fulani wajen aikata garkuwa da mutane.
A cewarsa, bawa irin wadannan Fulani ilimin addini ko na zamani shine kadai mafita daga kangin jahilcin da ya jefasu cikin irin mummunar rayuwa.

