Site icon Muryar 'Yanci

Ka Da Wanda Ya Zo Mini Yawon Sallah – Buhari

Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya bu?aci al’ummar Musulmi da su gudanar da bukukuwan ?aramar Sallah a gidajensu saboda gudun ya?uwar cutar korona.

Shugaban ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da Garba Shehu mai magana da yawunsa ya fitar ranar Lahadi, yana mai cewa shi ma a gida zai yi Sallar Idi kuma babu gaishe-gaishen Sallah bayan haka.

“Iyalan shugaban ?asa da masu taimaka masa da ministocinsa da shugabannin tsaro da ke zaune a Abuja za su yi sallar cikin bin dokokin kariya daga cutar korona a Fadar Shugaban ?asa,” in ji sanarwar.

“Bayan haka babu wata gaisuwar Sallah da za a yi.” Sanarwar ta ?ara da cewa za a tayar da sallar da ?arfe 9:00 na safe.

“Kamar yadda aka yi a bara, Buhari ya bu?aci shugabanni su gudanar da bukukuwa a gidajensu saboda annobar.”

A jiya Lahadi Buhari ya halarci rufe tafsirin Al?ur’ani mai girma da aka yi a fadar tasa, wanda Sheikh Abdulwahid Abubakar Sulaiman ya jagoranta tun daga farkon azumi.

Exit mobile version