Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da kwamitin kwararru mai mutum 27 kan aiyukan jinkan alummar kasa (NHCTWG) domin samar da goyon bayan kwararru ga kwamitin kula da aiyukan jin kai na kasa (NHCC) wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa domin kula da dukkanin aiyukan jinkai da agaji a fadin kasar nan.
Ministar harkokin Jinkai, kula da ibtilai da bunkasa walwalar jamaa Hajiya Sadiya Umar Farouk ita ce ta kaddamar da kwamitin, da samar da tsare-tsaren da suka dace domin kyautata aiyukan jinkan alumman Nijeriya da irin aiyukan da kwamitin zai gudanar.
Sadiya ta kalubalanci mambobin kwamitin da su tabbatar da aiwatar da dukkanin shawarorin NHCC da suke da alaka da tsarin CiSEC don fitar da tsararren tsarin gudanar da aiki tare da kaidoji gami kuma da sanya hangen nesa kan aiyukan da suka shafi jin kai da tallafa wa alumman Nijeriya.
Bugu da kari kuma, ta ce baya ga shiyyar arewa maso gabas, akwai bukatar kwamitin ya kuma yi laakari da dukkanin fadin kasar nan wajen gudanar da aiyukansa da suka dace.
Ta kuma nemi kwamitin da ya shigo da dukkanin wadanda abun ya shafa musamman wadanda suke da wani sani kan shawo kan rigingimu tare da lura da batun tsaro da ya shafi kasa.
A cewar Ministan tabbatar da samar da aiyukan hadaka da maaikatarta da bangarorin tsaro zai yi matukar taimaka musu wajen sauke nauyin da ke kawunansu na tallafa wa alumman Nijeriya har ma da rage kaifin fadawa cikin balaoi ta fuskacin kula da kayayyakin da aka samar da wadanda ake raba wa alumman kasa.
Kwamitin wanda Grema Ali ke shugabanta, ya kuma kunshi kwamishinonin da suke kula da bangaren jinkai da tallafa wa alumma na jihohin Borno, Adamawa da jihar Yola; shugabanin SEMA, NEDC da NCFRMI; hadi da wakilan soji, hukumar tarayyar Turai, hukumar raya kasashen duniya da kuma ofishin kasar Amurka kan kula da aiyukan jinkai.
Kwamitin ya sha alwashin gudanar da aiyukan da aka daura masa domin tabbatar da bada goyon baya da agajin kwarewa kan yadda za a tafiyar da aiyukan da suka shafi agaji da jinkai ga alumman Nijeriya.

