Site icon Muryar 'Yanci

Jigawa: Gujungu Ne Za?in Mu – Jama’ar Ringim Da Taura

An bayyana ?an takarar kujerar ?an Majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomi Ringim da Taura dake Jihar Jigawa Alhaji Gambo Ibrahim Gujungu a matsayin wanda ya zarce tsara kuma shi ne fata ga jama’ar yankin.

Al’ummar kananan hukumomin Ringim da Taura ne suka bayyana hakan a wata tattaunawa da suka yi da Wakilinmu da ziyarci yankin a ranar Juma’a.

Sun bayyana yankin nasu a matsayin wanda ya dade cikin koma baya sakamakon rashin samun kyakkyawan wakilci, amma cikin ikon Allah samun Gambo Ibrahim Gujungu cikin ‘yan takara ya sanya sun samu karsashi da ganin wanda zai kai yankin nasu ga nasara.

A zantawar da ya yi da Wakilinmu ta wayar tarho Gambo Ibrahim Gujungu ya bayyana cewar damuwa da kishin jama’ar yankin nasu ne ya sanya shi fitowa takara domin bada gudunmawa na ciyar da yankunan gaba.

Exit mobile version