Furodusa kuma mai wasan barkwanci na masanaantar Kannywood, Malam Habu wanda aka fi sani da Mazaje, ya yi kira da a daina sa duk wata jarumar masanaantar da ta yi aure, sannan aurenta ya mutu ta dawo masanaantar.
A wani dan karamin bidiyo da ya fitar, Mazaje ya ce, duk wani furodusa ya sake wata ta fito a aure ya saka ta a fim, ni babu abin da zan ce masa, sai wuta balbal.
Sannan ya rubuta a saman bidiyon cewa, duk wata jarumar Kannywood da ta yi
aure ta fito aka sata a film, wuta balbal.
Sai dai wani mai suna Imrana CMC ya mayar masa da martani, inda ya ce, to kai a su wa a Kannywood? Kai da dan wasan barkwanci ne. Mazaje ba ka iya magana ba, watarana bakinka shi zai jawo a daure ka. Ka bi a hankali.
Mazaje shi ne forodusan fim xin Daga wasa mai dogon zango da yanzu haka ake haskawa a YouTube.

