Abin ba?in ciki da alhini ya samu jamiyya mai Mulki ta APC inda ta rasa daya daga cikin manyan jiga-jiganta a Shiyyar Kudu maso yammacin Najeriya, mai suna Mista Samuel Ojebode.
Tuni Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ta hannun mai magana da yawun shi Femi Adesina ya aike da sa?on ta’aziya ga iyalai da ‘ya’yan jam’iyyar APC bisa ga wannan babban rashi da ya faru.
Ojebode, wanda ya kasance jigon APC a jihar Oyo, ya rasu a ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamba, yana da shekaru 87 a duniya. A wani sakon taaziyya, da wani sanata daga jihar, Teslim Folarin ya wallafa, ya nuna bakin cikinsa, da ki?imewa akan wannan rashi.
A wani jawabi daga Yakeeen Olaniyi a Ibadan, Folarin ya bayyana mutuwar a matsayin wani babban asara ga ahlin APC a Najeriya.
Folarin ya bayyana cewa jigon na APC ya shirya taro na lumana mai cike da nasara ga ‘ya’yan jamiyyar a mazabar Oyo ta tarayya.
Ya ?ara da cewar Ojebode ya kasance shugaba abun koyi, mai mutunci da kima.
A sakon taaziyyar shi Farfesa Adeolu Akande, Shugaban hukumar NCC, ya yi taaziyya ga iyalai, abokai da ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar kan wannan rashi.

