Mawallafin jaridar nan ta Daily Nigeria Jaafar Jafar, ya ce duk da bukatar janye ?arar da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kai shi a babbar kotun jihar, ba zai dawo kasar ba har sai ya samu tabbacin kare lafiyarsa daga rundunar yan sandan kasar.
Jaafar Jaafar da ke zaman mafaka a Birtaniya ya ce, janye shariar wata manuniya ce da ke cewar wata?ila gwamanan na Kano ya fahimci gaskiya.
“Tabbas ba zan dawo Najeriya ba har sai na samu tabbacin kariyar lafiyata da ta iyalina”

