Site icon Muryar 'Yanci

Iran Ta Damke Shahararriya Jarumar Fina-Finan Kasar

An kama tauraruwar fim Taraneh Alidoosti a Iran yayin da zanga-zangar ?in jinin gwamnatin ?asar da ake yi ta shiga wata na hu?u.

Kamfanin dillancin labarai na kasar ya ce an kama jarumar ne bayan ta wallafa wani sako da hukumomi suka kira na ?arya da kuma ?okarin tunzira masu zanga-zanga a shafinta na sada zumunta.

Shahararriyar da ta samu lambobin yabo da dama ta yi Allah-wadai da hukuncin kisan da aka yanke wa wani mai zanga-zanga a farkon watan nan.

A makonnin baya, ‘yar fim ?in ta sanya wani hotonta a shafin sada zumunta babu ?an-kwali tana kuma rike da allon alamar nuna goyon bayan zanga-zangar da ake yi a kasar.

Tauraruwar ta fito a cikin fim din da ya yi fice mai suna The Salesman.

Exit mobile version