Hukumar za?e mai zaman kanta ta ?asa INEC, ta ce ta yanke shawarar tura ?arin na’urorin yin rajistar za?e a wasu jihohi saboda cunkoso da ake samu a wuraren da ake ?orafe-?orafe.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Juma’a ta ce ta lura cewa an fi samun cunkoson a jihohin Kano da Legas da kuma yankin Kudu maso Gabas, inda ta tura ?arin na’urorin 209.
“Hukumar za ta ci gaba da sa ido kan aikin na tsawon kwanaki sannan ta sake duba ci gaban da aka samu,” a cewar INEC.

