Shugaba Muhammadu Buhari ya ce cin hanci da rashawa ya kasance babbar barazana da ?asashe ke ci gaba da fuskanta.
Ya bayyana haka ne jiya a fadarsa da ke Abuja, yayin da ya kar?i bakuncin shugabannin gudanarwar Kotun ?aar Maaikata karkashin jagorancin shugabanta, Danladi Yakubu Umar.
Buhari ya ce yana fatan irin kokarin da gwamnatinsa ta yi wajen yaki da cin hanci da rashawa, ita ma gwamnati mai zuwa za ta ?ora a kan haka.
Ya bayyana Kotun ?a’ar Ma’aikata a matsayin muhimmiya ce wajen yaki da rashawa da gwamnatinsa ta yi cikin shekaru bakwai da suka gabata, inda ya ce irin wa?annan hukumomi suna taimakawa gwamnati wajen yaki da masu satar dukiyar ?asa.
“Muna fata cewa irin tubali ko kokari da ta yi a ?angaren yaki da rashawa ya zama mai zuwa ta ?ora kan haka saboda yadda hakan ke barazana ga ?asashe,” in ji Buhari
Buhari ya kuma gode wa Kotun ?a’ar Ma’aikatan saboda irin sadaukarwa da ta yi duk da irin matsin tattalin arziki da kuma raguwar ku?a?en shiga da gwamtai ta samu,” inda ya yi alkawarin samar da sabbin tsare-tsare da za su samar da ku?ade ga hukumomin wa?anda ya ce suna da matukar muhimmanci.
Shugaban Kotun, Danladi Umar ya yaba wa gwamnatin Buhari kan irin rawar da ta taka a fannin raya ababen more rayuwa da noma da kuma samar da ayyukan yi da sauransu.

