Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce yana da tabbacin Shugaba Muhammadu Buhari zai cika alkawarin da ya yi na kawo karshen rashin tsaro a arewa.
Gwamnan ya fadi haka ne a wata sanarwa da shi da kan sa ya sanya wa hannu, kuma aka rarraba ta ga manema labarai a Abuja.
Matawalle ya ce yayin ganawa da shugaban kasa, gwamnoni daga jihohin arewa sun yi ta bayyana halin da suke ciki, abubuwan da suke fata daga gwamnati, da kuma kokarin samar da mafita mai dorewa.
Ya ce gwamnonin arewa sun dukufa wajen tallafawa kokarin shugaban kasa na kawo karshen matsalolin tsaro a kasar kuma suna samun gamsuwa daga matakan da shugaban ke dauka.
Matawalle ya yi kira ga fitattun mutane da sauran yan siyasa, musamman daga arewacin Najeriya, da su kasance masu hadin kai tare da fuskantar kalubalen da ke lalata ci gaban yankin da ci gaban sa.
“Shugaban kasar ya ba da tabbacin cewa zai kawo karshen matsalar tare da mayar da yankin da kuma kasar baki daya ga abubuwan da suka rasa. Lokaci ya yi da zamu kawo karshen barna da kashe-kashe, mu koyi halaryar yafewa laifinmu, mu nisanci rarrabuwar kawuna sannan mu zama masu hadin kai.
Za mu ci gaba da mai da hankali ga ci gaban kasa tare da yin watsi da banbancin siyasa ba tare da laakari da jamiyyar da muke ciki ba, inji shi.
Matawalle ya yi kira ga shugabanni da su ci gaba da jan hankulan mutane game da hanyoyin da suka dace da kuma ci gaban kasar Najeriya wadda bamu da wata kasar da ta fita.
“Dole ne shugabanni su yi shawarwari kan mafita, su guji son kai don kawo karshen kashe-kashe da barnata rayuka dukiyar ‘yan ?asa.

