Site icon Muryar 'Yanci

Ihun Masu Ihu Ba Zai Sa Buhari Sauka Daga Mulki Ba – Fadar Shugaban Kasa

Fadar Shugaban Kasa ta mayar da martani akan kiraye kirayen da wasu mutane ke yi na cewar wai Shugaban ?asa ya sauka daga Karagar Mulki, saboda abin da suke gani na gazawarshi ta fuskar samar da tsaro tun bayan mummunan kisan da Boko Haram ta yi wa Manoman Shinkafa 43 a kauyen Zabarmari dake ?aramar Hukumar Jere ta Jihar Borno makon da ya gabata

Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa duk da kiraye-kiraye da ake yi na yayi murabus.

Da yake magana a wajen waata ganawa da kungiyar mamallakan jaridun Najeriya (NPAN) a Lagas a ranar Alhamis, Lai Mohammed ya ce kira da ake na Shugaban kasar yayi murabus siyasa ce kawai.

Ministan ya bayyana bukatar Shugaban kasa yayi murabus kafin kammala wa’adin mulkinsa saboda kisan wasu manoma a jihar Borno a matsayin rashin tunani da wata adawa mara fasali.

“A na tsaka da lamarin kashe-kashe, ?angaren jami’an tsaro na bakin kokarin su, sannan wasu marasa kishi kiran Shugaban kasar yayi murabus.

“Don haka, bari na fadi cewa wannan kira shiri ne na buga kazamar siyasa da lamarin tsaro, kuma hakan rashin tunani ne. An zabi Shugaban kasar a 2015 na tsawon shekaru hudu sannan aka sake zabarsa a 2019 don ya sake wasu shekaru hudun.”

Ya jaddada cewa babu wani ihun da za a yi masa na yayi murabus da zai hana Shugaban kasar cike wa’adinsa. Ministan ya ce kokarin janye hankali da kazamar siyasa ce ke sa ake neman Shugaban kasar ya sauka daga mulki a duk lokacin da aka samu akasi a yaki da ta’addanci.

A baya dai mun ji cewa, kungiyar dattawan arewa ta sake sabonta kiran da take yi na neman Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi murabus.

Da yake magana a yayin hira da Channels Television a ranar Laraba kakakin kungiyar, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce hujjojin da ke kasa sun marawa kiraye-kiraye da suke yi ga Shugaban kasar yayi murabus.

Ya ce: “Hujjar da ke kasa ya marawa abunda muke fadi baya. Shugaban kasar ya yi rantsuwa da Al-Qur’ani don kare al’umman kasar. Ya gaza yin hakan. “Wannan shine shekararsa ta biyar a kan mulki. Halin da ake ciki yana kara tabarbarewa a karkashinsa kuma babu alama da ke nuna abubuwa za su inganta.”

Exit mobile version