Site icon Muryar 'Yanci

Hukumar Zabe Ta Sanya Ranar Za?en 2023

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin taron yini ?aya na sauraren dokar laifukan Zabe ta 2021, wanda kwamitin Majalisar Dattawa kan INEC ya shirya.

“Bisa dokar da aka kafa hukumar, za?en 2023 zai kasance ranar Asabar 18 ga watan Fabrairun 2023, wanda ya rage saura shekara ?aya da wata Tara da mako biyu da kwana shida daga yau.”

Shugaban Hukumar ya ce suna fatan tsara jadawalin za?en da zarar an kammala za?en gwamnan jihar Anambra wanda za a gudanar a ranar 6 ga Nuwamban 2021.

“Don yin yin hakan, ya kamata a samu tabbaci game da tsarin dokokin za?e don gudanar da za?en. Muna da yakinin cewa Majalisar Tarayya za ta yi abin da ya kamata cikin lokaci,” in ji shugaban INEC.

Ya ce Hukumar ta matsu ta san tanadin doka da zai jagoranci gudanar da babban za?en na shekarar 2023.

Tanadin INEC a za?en 2023

Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi hasashen cewa yawan masu rajistar za?e a Najeriya za su iya kai miliyan 100 kafin babban zaben 2023.

Shugaban na INEC wanda ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da hukumomin ?asashen waje da suka ha?a da hukumar raya ?asa ta Amurka USAID a Abuja ya ce za a ci gaba da yin rijistar masu za?e daga 28 ga watan Yunin bana har zuwa ?arshen 2022.

“Wadanda suka yi rijistar za?en 2019 sun zarta miliyan 14, adadin zai ?aru a za?en 2023 inda wa?anda suka yi rijistar za?e za su iya kai wa miliyan 100 ko fiye da haka,” in ji shi.

Hukumar INEC ta kuma ce za ta fa?a?a runfunan za?e domin sawwake za?en ga ?an ?asa. Ta ce runfunan da ake da su tun shekara 25 ne ba a ?ara ba.

Exit mobile version