Hukumar Raya yankin Arewa maso gabas ta kaddamar da aza tubalin gina gidaje kimanin dari biyar a Jihar Bauchi, a wani yunkuri na rage matsalar karancin gidajen zama a dukkanin jihohin da suka fito daga yankin baki daya.
Shugaban hukumar wanda yake bayanin makasudin wan nan tallafi na gina gidaje da kayan tallafin abinci da na amfanin yau da kullon ga numbin wadanda matsalar tsaro da na ambaliyan ruwa da ta shafa,
A wajen taron aza harshen ginin gidajen da ya gudana a cikin karamar hukumar Bauchi, a kauyen dungal a gefen hanyan zuwa Jos daga Bauchi, yace hakan ya faru ne tare da goyon bayan gwamnatin Jihar domin rage ma al’umma matsalolin rayuwa a fadin Jihar.
A lokacin da yake Jawabinsa Gwamnan Jihar Bala Abdulkadir Mohammed ya yaba da irin kokarin da hukumar take yi a jihohin yankin musamman a Jihar Bauchi.tare da godewa Shugaban kasa muhammadu Buhari kan kirko wan nan hukuma da kuma yan’majalisun tarayya don bada tasu goyon bayan kan ci gaban arewa maso gabas da rashin tsaro ya daidaita.
Har’ila yau Gwamna Bala yace a matakin jiha tuni gwamnatinsa ta himmatu wajen rage ma mutanen da Ibtila’i ya ritsa dasu ko ma tsaro ko na ambaliyar ruwan sama a wasu wurare, ukubar da suka sami kansu, Kuma ya jaddada aniyar sa na bada tallafin kayan abincin da sauransu sun kai inda ya kamata.
Sanata Yusu A Yusuf Shugaban kwamitin na musamman a majalisar tarayya yace dukkanin su a matakin majalisar sun amince da irin ayyukannda hukumar ke gudanarwa tare da basu dukkannin wani goyon baya.
Ita ma Shugaban kwamitin Raya yankin Arewa maso gabas Hajiya Khadija Bukar Ibrahim Wanda dannmajalisar tarayya daga NIngi Abdullahi Sa’ad ya wakilce ta, ta Yaba ma Gwamnan Bauchi da irin kokarin sa na bunkasa tattalin arzikin al’ummar Jihar Bauchi, birni da kauye, tace ya Zama ala tilas a hada karfi da karfe donnceto yankin ta ayyukan more rayuwa da na hukamar duk wani goyon baya da ya kamata.
Daga Adamu Shehu Bauchi

