Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar yi wa kasa hidima ta NYSC ta sanar da aniyarta na hadin gwiwa da kungiyar yan wasan kwaikwayo na Najeriya (AGN) kan zakulo kwarewar mambobinta a fannin shirya fina-finai.
A cewar kamfanin dillancin labarai na NAN, Shuaibu Ibrahim, babban daraktan NYSC, ne ya bayyana haka a ranar Laraba 8 ga watan Satumba lokacin da ya karbi bakuncin Emeka Rollas, shugaban AGN, a ofishinsa da ke Abuja.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Adenike Adeyemi, mai magana da yawun NYSC, Ibrahim ya ce tun lokacin da aka kafa shirin a shekarar 1973, NYSC ta bai wa membobinta damar samun sanaoi masu kyau a masana’antar nishadi.
Wannan kenan ta hanyar shirye-shiryen ta da ayyuka daban-daban. Daya daga cikin irin wadannan shirye-shiryen a cewarsa shi ne bukukuwan wasanni da al’adu wadanda shirin ke shiryawa a duk shekara.
Shirin NYSC ya kirkiri bukukuwan al’adu a shekarar 2020 domin zakulo matasa masu basirar harkar wasan kwaikwayo su shiga cikin shirin na shekara-shekara. A cewarsa, wannan yunkuri na NYSC zai habaka hanyoyin samar da kudin shiga ga hukumar NYSC, ‘yan bautar kasa da ma kasa baki daya.
Shugaban ya kuma umarci AGN da ta hada gwiwa tare da shirin don zakulo membobin bautar kasa da za su iya yin kafce, bada umarni, tsara labari, da sauran fannonin shirya fim. Ibrahim ya kara da cewa: “Lokacin da aka fara aikin, hadin gwiwar za ta haifar da tsarin zabi gwanaye a sansani daban-daban na NYSC kuma za ta kai ga babban wasan karshe, inda za a zabi mafi kwarewa kuma a tura shi zuwa Kungiyar ‘Yan Wasan Kwaikwayo na Najeriya.”

