Site icon Muryar 'Yanci

Hukumar ICPC Na Neman Surukin Buhari Ruwa A Jallo

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta ayyana neman Gimba Yau Kumo, surukin Shugaba Muhammadu Buhari ruwa a jallo kan zargin damfara ta Dala Miliyan 66 $66m.

A sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis, Azuka Ogugua, mai magana da yawun hukumar ya ce ana neman Kumo da Tarry Rufus da Bola Ogunsola ruwa a jallo kan zargin ?annatar da karkatar da kudaden shirin samar da gidaje na ?asa.

Kumo, tsohon shugaban Bankin Samar da Gidaje na Nigeria, ya auri, Fatima, ?ar shugaban ?asa a 2016 a Daura, jihar Katsina.

“Hukumar yaki da rashawa ta ICPC na neman mutane uku da aka saka hotunansu ruwa a jallo, Mr Gimba Yau Kumo, Mr Tarry Rufus da Mr Bola Ogunsola kan ?annatar da ku?i na Hukumar Samar da Gidaje na ?asa da karkatar da Fam miliyan 65 ($65,000,000), a cewar ICPC.

“Duk wani da ke da bayani mai amfani game da su ya kai rahoto hedkwatar ICPC da ke Abuja ko kuma duk wani ofishin ICPC na jihohi ko ofishin yan sanda mafi kusa.”

A watan Afrilu, kwamitin majalisar Dattawa na binciken yadda ake kashe kudaden gwamnati ta gayyaci Kumo domin ya yi bayani zargin rashin ?a’ida da aka bi wurin bada kwangilar Naira biliyan 3 a lokacin da ya ke bankin.

Exit mobile version