Site icon Muryar 'Yanci

Hujjojin Cancantar Abdulaziz Yari A Mukamin Shugaban Majalisar Dattawa – Dambatta

Me ya sa har yanzu ka dage akan goyon bayan Sanata Abdulaziz Yari bayan jam’iyyar APC Ta bayyana goyon bayanta ga Sanata Akpabio?

Dambatta: Da fari dai ya kamata a sani Sanata Yari ?an takara ne wanda ya fito daga shiyyar Arewa maso yamma wanda yake da tarihi na gogewa da kuma kwarewa a siyasa, Sannan abu na biyu shiyyar Arewa maso yamma bisa ga lissafin kuri’un za?e ita ce shiyyar da ta fi kowace shiyya a ?asar kawo yawan ?uri’u, domin ta samar da kaso 30 cikin 100 na kafatanin kuri’u a ?asar.
Ka da mu mance da cewa za?a??en shugabab ?asa ya samu adadin kuri’a Miliyan 8.79, wannan shine dalilin da ya sa shiyyar Arewa maso yamma ta zama jagaba na yawan ?uri’un da aka jefa. Duk da cewar shiyyar da Tinubu ya fito ta kudu maso yamma ta samar da kashi 25.9 inda ta zo a matsayin ta biyun sannan shiyyar Arewa ta tsakiya ta zo a ta uku da kashi 20, sannan shiyyar Arewa maso gabas ta zo ta hu?u da kaso 13.5.
Shiyyar kudu maso kudu ta zo ta biyar da kashi 9.10 sannan shiyyar kudu maso gabas ta zo a matsayin ta shidda da kashi 1.45 duka a bisa sikeli na hukumar zabe wanda hakan kai tsaye ya tabbatar da cancantar Yarin wanda ya fito daga shiyyar Arewa maso yamma akan kowa.

Wannan shine babban dalilin da ya sa kungiyar mu ta cigaban yankin Arewa maso yamma muke kira ga za?a??en shugaban kasa Tinubu da cewar ya martaba wannan gata da yankin ya bashi ta hanyar mara wa Abdulaziz Yari baya.
Muna da tabbaci da yakinin cewa Yari shine mafi cancanta akan dukkanin ‘yan takarar da suka fito. Matsayinmu akan haka shine nasarar APC a za?e zai yi tagomashie ne idan aka martaba zabin da jama’a suka yi wanda kowa ya sani zabin jama’a shine jagorancin Abdulaziz Yari a majalisa.

Mun gani gwamnonin yankin kudu maso yamma inda Tìnubu ya fito sun yi watsi da matakin da APC ta dauka, sannan gamayyar kungiyoyin arewa (CNG) sun yi gargadi akan abin da suke gani hawan kawara akan shugabancin majalisa. Labarin bai canza zani ba ta bangaren majalisar wakilai ?ar?ashin jagorancin Gbajabimila, yanzu ya bayyana a fili matakin da APC ta dauka bai wadatar ba.

Ta Wane ?angare Ka Ke Ganin Yari Ya Fi Dacewa Da Cancanta Akan Sanata Akpabio Dake Orji Uzor-Kalu?

Sanannen abu ne cewar Yari ya da?e cikin Jam’iyyar APC Shekaru da dama wanda gudummawar da ya bayar ta taimaka wajen samun nasarar kafuwar APC.
Ka da mu mance Yari babban jigo ne a siyasa tun zamanin da ake jam’iyyar ANPP, ya fito kasance Sakataren jam’iyyar wanda ya taka rawa wajen dinke duk wata barakar jam’iyyar a Zamfara lokacin da zafin siyasa ya yi ?amari a yankin, ya rike jagorancin Jam’iyyar har ya yi nasarar dawo da tsarin karfinta a jihar. Don Allah ka bincika daga ?angarenka ka sanar dani a wane lokaci Sanata Akpabio ya shigo jam’iyyar APC? Yaushe Sanata Uzor-Kalu ya shiga APC? Ka ga a siyasa da?ewa a bauta ‘yanci ne, amma ina tabbatar maka Yari ya taimaki jam’iyya fiye da yadda ake zato ya zama wani jigo da ya taimakawa jama’ar Zamfara wajen ciyar da su gaba, wannan a fili yake ko bayan da ya bar mu?amin Gwamna bai jefar da jama’arsa ba wannan shine dalilin da ya sa ya lashe zaben Sanata da gagarumin rinjaye, ba na tunanin da akwai wata kamanceceniya wadda za a iya ha?a cancantar Abdulaziz Yari da Akpabio ko Uzor-Kalu.

Wadanne Hujjoji Ka Ke Dasu A Hannu Da Za Su Tabbatar Da Abin Da Ka Ke Fadi Akan Yari Na Cancanta Bayan Kasancewar Wannan Shine Karon Shi Na Farko Da Zuwa Majalisar Dattawa?

Batun cewa wannan shine zangon shi na farko a majalisa wannan ba wani abun damuwa bane, idan aka yi la’akari da irin nasarar da wasu Sanatocin suka samu a zangon su na farko, bari in baka misali da za?a??en gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani wanda a zuwanshi Majalisa a zangon farko ya yi abin da Tsofaffin Sanatoci ba su yi ba, ya gabatar da manyan kudurori da dokoki sama da 30 a ?asa da shekaru 2. Ka kalli yadda kudirin da ya gabatar na gyaran fuska akan tsohuwar dokar banki ya zama kudirin doka na farko da Buhari ya sanya wa hannu.
Akwai Sanatoci da dama ‘yan zangon farko wanda sun taka rawar ciyar da ?asa gaba da da?a??un Sanatoci ba su taka ba. Yanzu idan ka kalli Sanata Tambuwal wannan shine zangon shi na farko a majalisar Dattawa duk da cewa a baya ya jagoranci shugabancin Majalisar wakilai, haka abin yake a bangaren gwaninmu Abdulaziz Yari ya kasance gagarabadau a zamanin da yake Majalisar wakilai sannan yanzu yana matsayin Sanata, wannan shine da yasa mu a kungiyance abin da muke kallo shine manufarka ga Jama’a ba wai dadewa a majalisa ba.

Ba Ka Ganin Shugabancin Yari A Majalisa Zai ?ara Haifar Da Cece-Kuce Akan Batun Tikitin Musulmi Da Musulmi

A kungiyance abin da muke kallo shine abin da dokar ?asa tace na ha?akar ra’ayoyin Majalisa. Babu wani wuri da kundin tsarin mulki ya yi magana akan ba da shugabanci na da ala?a batun addini ko ?abila, babu wani Ofishin Siyasa ko wani matsayi a Najeriya da ya ware cewa dole sai mabiyin addini kaza ne za a ba, abin da ya ke a zahiri shine batun daga wane yanki ko sashi Mutum ya fito.
Babu batun wane Musulmi ne ko Kirista ne a batun harkar siyasa ko za?e.

Wane Tabbaci Ka Ke Dashi Akan Cewa Shugabancin Yari A Majalisa Zai Bambanta Da Irin Wanda Muke Gani Tun Daga Shekarar 1999?

Kungiyar mu ta mayar da hankali ne wajen tabbatar da ganin samun nasarar dimukura?iyya da adalci ga kowa, muna da tabbacin dukkanin abubuwan da ake nema ga shugaba Abdulaziz Yari na dasu, tabbas idan aka za?i Yari a matsayin shugaban majalisar Dattawa ?asa za ta kai ga tudun mun tsira.

Exit mobile version