Site icon Muryar 'Yanci

Hauhawar Rashin Tsaro: Jinina Na Hawa A Kowace Rana – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana matukar shiga takaici da bakin ciki, wanda ke sanya jinin shi ke hawa in har aka samu rashin zaman lafiya da karantsaye a kan tsaro a kasar nan.

Shugaban kasan a sakonsa na Kirsimeti ga ‘yan Najeriya ya yi kira garesu da su bada goyon baya ga dakarun soji da sauran hukumomin tsaro.

“Da gangan ba zan ki sauke babban nauyin da ke kaina ba na tabbatar da tsaron rayuka da kadadrori ba. Ina shiga halin takaici matukar aka samu karantsaye a fannin tsaron kasar nan.

“Na kan shiga halin damuwa fiye da matasa. A yanzu an fi saka wa ‘yan makaranta ido kuma ‘yan ta’addan nan suna mayar da su hanyar tada hankulan al’umma.

“A matsayina na uba, ina samun tashin hankali tare da alhinin da iyaye tare da marika ke shiga idan yaransu suka fada hannun makiyan al’umma.

Ya dauka alwashin cewa gwamnatinsa za ta cigaba da bai wa dakarun soji dukkan goyon baya da suke bukata.

Ya horesu da su mayar da hankali wurin kawo karshen rashin tsaron da ya addabi jama’a.

Exit mobile version