Rahoton dake shigo mana daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sufeto Janar na Yan Sandan Najeriya Usaman Al?ali ya ce ana samun wanzar da tsaro bakin gwargwado, a Najeriya duk da irin kalubalen da ake fuskanta jefi-jefi.
Alkali Baba ya ce a ?ar?ashin sa zaratan yan sanda na bakin ?o?arin su na tabbatar da wanzuwa da ?orewar zaman lafiya da zaman tare a fa?in ?asar nan
Al?ali ya yi wannan bayani ne a ranar Alhamis, lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a Fadar Shugaban ?asa, yayin taron sa da yan jarida.
Sai dai kuma wannan i?irari da Sufeto Janar Al?ali ya yi, ya zo ne daidai lokacin da ake ta samun ?aruwar kashe-kashe da tashe-tashen hankula a sassa daban-daban na ?asar nan.
Sau da yawa kuma ana ?orafi cewa ko an kira yan sanda domin kai agaji a inda aka kai hari, ba su zuwa sai bayan awa ?aya da tafiyar mahara, bayan sun yi kisa, sun kuma kwashi wa?anda za su yi garkuwa da su.
Sama da mutum 200 yan bindiga su ka bindige a cikin makonnin da su ka shige.
Sai da kuma IGP Al?ali ya ce rundunar sa na nan na sake nazarin tsarin samar da tsaro a cikin alumma, domin magance abin da ya kira, rikice-rikicen da ake samu a cikin jamaa, cikin sassan ?asar nan.
Shirin samar da tsaro na ha?in-guiwa tsakanin yan sanda, sojoji da sauran ?angarorin jamian tsaro, ya na ?arfafa tsaro sosai da sosai
Ya ce ana nan ana ta ?ara zaratan yan sanda a wuraren da ake da barazanar matsalar tsaro da yawa.

