Site icon Muryar 'Yanci

Harin ‘Yan Bindiga Ya Tilasta Rufe Kwalejin Kimiyya Da Fasaha Ta Nuhu Bamalli

Hukumar Kwalejin Nuhu Bamalli da ke Jihar Kaduna ta sanar da rufe makarantar sakamakon harin ‘yan fashin daji da ya yi sanadiyyar kashe ?alibi da kuma sace wasu guda takwas.

Da daren Alhamis ne ‘yan bindigar suka afka makarantar, inda suka kashe ?alibi sannan suka yi garkuwa da malamai biyu da kuma wasu ?aliban guda takwas.

Mazauna yankin sun ce maharan sun dinga harbi a kan kowa da kowa domin korar mutane.

Wata sanarwa da ofishin ya?a labaran kwalejin ya fitar ta umarci dukkan ?alibai da su zauna a gida ban da ‘yan sashen IJMB wa?anda ke shirin fara jarrabawa ranar Talata mai zuwa.

Lamarin na zuwa bayan wasu ‘yan bindiga sun sace mata 60 a Jihar Zamfara da ke yankin na arewa maso yammacin Najeriya a farkon wannan makon.

Har yanzu masu satar mutane don neman ku?in fansa na ri?e da ?aliban Islamiyya kusan 136 da suka sace a makarantar Salihu Tanko da ke JIhar Neja mai ma?otaka da Abuja, babban birnin ?asar.

Exit mobile version