Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?an bindiga da suka kai harin bam a jirgin ?asa a hanyar Abuja zuwa Kaduna sun saki shugaban bankin manoma Alwan Ali Hassan ?aya daga cikin fasinjojin da suka yi awon gaba da su a cikin jirgin.
An sake shi ne a ranar Laraba, kamar yadda wata majiya daga iyalinsa ta tabbatar wa BBC.
A ranar Litinin 28 ga watan Maris ?an bindiga suka kai harin bam a jirgin ?asa da ke kanyar zuwa Kaduna daga Abuja.
Hukumar kula da sufurin jiragen ?asa ta ce jirgin na ?auke da fasinja 362, kuma har yanzu ba a san makomar sama da 160 bayan tabbatar da mutum 182 da suka tsira.

