Rundunar Sojin saman Najeriya sun musanta i?irarin da ?an ?ungiyar boko haram suka yi a wani bidiyo na harbo jirgin ya?in sojojin da aka nema aka rasa tun ranar Laraba, 31 ga watan Maris.
Kamar yadda kafafen Jaridu suka wallafa, Boko haram sun saki wani bidiyo suna tabbatar wa da duniya cewa sune suka harbo jirgin ya?in.
Sai dai babban jami’in hul?a da jama’a na sojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ya musanta maganar wannan bidiyon da ?an Boko Haram suka saki.
Ya ?ara da tabbatar wa da duniya cewa ?an Boko Haram sun lailayo wata ?aryar ne kawai suka maka duk don su ?ara wa labarin armashi amma maganar gaskiya ba haka bane.
Kamar yadda kakakin NAF din, Air Commodore Edward Gibkwet yace: “Mun ga wasu bidiyoyi suna yawo wadanda babu wata alama da take nuna cewa jirgin namu ne, ko kuma wani matu?in jirginmu ko kuma alamar jirginmu ne wannan wanda suke nunawa.
“Da alama wani bidiyo ne can daban da aka ?auka a wani wuri wanda ko shuke-shuken wurin ba na arewa maso gabas bane. Suna ta sakin bidiyoyin da kadan-kadan kuma muna kallo.”

