Fitacciyar jarumar masana’antar Nollywood, Bimbo Akinsanya wacce aurenta ya mutu lokacin tana da yaro mai wata uku a shekarun baya da suka gabata, tace ta mayar da hankali kan fim a yanzu fiye da batun aure.
A tattaunawarta da jaridar Vanguard, tace tana kokarin ganin ta ba wa ‘danta lokacinta wanda hakan ke da matukar muhimmanci.
Tantancewa nake yi, har yanzu ban ga nagartaccen namijin da ya dace da ni ba, ta bayyana yadda take kula da ‘danta ita kadai ba tare da tallafin uban yaron ba.
“Ba abun wasa bane kula da ‘da kai kadai babu wani tallafi. Tunda na rabu da mahaifinsa, ban taba samun wani tallafi na kula da yaron ba har yanzu.”
“Ban taba nadamar rabuwa da mahaifin ‘da na ba. Barin gidan aure da yaro mai wata uku kun san an kai mace bango ne.” Tace idan zata yi aure, sai ta tankade tare da rairaye wanda zata aura domin samun nagartaccen miji.
“Zan lura da komai da idon basira tun muna soyayya kafin aure. Ba nan kawai ba, zan duba irin gidan da ya fito, don wasu a tarbiyarsu babu kauna da tausayi kamar yadda ake tarbiyantar da yara nagari.
Duk da shekarunta 52, ta bayyana cewa tana da manema da yawa. “Sai dai, ina taka-tsan-tsan saboda abinda na fuskanta a baya. Akwai wasu irin nagartattun halaye da nake son namiji ya mallaka wanda har yanzu ban samu mai irinsu ba.

