Babbar Al?alin Jihar Kano, Dije Abdu-Aboki, ta sauya wa tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jamiyyar APC na ?asa, Abdullahi Ganduje sabon al?ali.
Tsohon gwamnan dai na fuskantar tuhuma ne tare da wasu mutane bakwai ciki har da matarsa Hajiya Hafsah Ganduje.
Kamfanin dillancin labarai na ?asa (NAN), ya ruwaito cewa ragowar wa?anda ake tuhuma sun ha?ar da Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash properties Limited, da kuma Safari Textiles Limited.
Kafin wannan sauyi dai ana gudanar da shariar ne a wata babbar kotu mai lamba 4, ?ar?ashin mai sharia Usman Naabba, amma yanzu ta koma babbar kotu mai lamba 7 ?ar?ashin mai sharia Amina Adamu Aliyu.
Mai magana da yawun hukumar sharia ta Jihar Kano, Baba Jibo-Ibrahim ne, tabbatar da wannan sauyi a yau Alhamis yayin wata tattaunawa da manema labarai.
Jibo, ya ce ofishin babban mai shariar yana da yancin yin hakan bisa doka.
Ana tuhumar shugaban jamiyyar APC da laifuffukan takwas da suka ha?a da cin hanci, almundahana, almubazzaranci da dukiyar gwamnati na biliyoyin Naira.
Sai dai kuma har bayan wannan sauyi ba a sanya ranar sauraren shariar ba a gaban Adamu-Aliyu.

