Site icon Muryar 'Yanci

Hajjin Bana: An Cimma Matsaya Tsakanin Gwamnati Da Kamfanonin Jigilar Alhazzai

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar hukumar alhazai ta kasa ta tabbatar da cewa ya?in da ake yi a Sudan zai shafi jigilar mahajjatan ?asar na bana.

Hakan kuma mai yiwuwa ne zai janyo a bu?aci maniyyata su biya ?arin ku?i.

A jiya ne, hukumar da kamfanonin sufurin jiragen sama na cikin gida suka rattaba hannun a kan yarjejeniyar jigilar mahajjatan ta bana.

A makon jiya dai sun gaza yin hakan saboda batun ?arin ku?i.

Sai dai hukumar ba ta bayyana ko matakin na nufin, maniyyata aikin hajji ne za su biya ?arin ku?in da dogon zagayen zuwa ?asa mai Tsarki ko a’a ba.

Abdullahi Magaji Hardawa, kwamishinan kula da tsare-tsare da gudanar da aikin Hajji a hukumar ya ce kamfanonin sufurin jiragen sama sun nemi sai an daddale kafin sanya hannu a kan yarjejeniyar.

Ya ce ba a cimma matsaya zuwa yanzu a kan ko mahajjata ne za su yi ?arin ku?in na jigilar aikin hajjin na bana ba.

A cewarsa, matu?ar ba a bu?e sararin samaniyar Sudan ba, har zuwa lokacin da aka fara jigilar mahajjatan bana daga Najeriya, hakan na nufin sai jiragen sama sun yi zagaye, abin da kuma tabbas zai haddasa ?arin ku?i.

Jami’in ya ce babban hatsari ne jirgin sama ya ce zai ratsa ta sararin samaniyar Sudan, abin da ya janyo su kansu hukumomin ?asar suka dakatar da zirga-zirgar jiragen sama ta sararin samaniyar Sudan ?in.

Har?awa ya ce matu?ar aka fara jigilar maniyyata aikin hajji na bana, ba tare da an bi ta samaniyar Sudan ba, za a fuskanci matsaloli guda biyu ko fiye.

“Na farko, in ba za a shiga ta sararin samaniyar Sudan ba, dole za a shiga ta wasu ?asashe. To ?asashen nan akasari, za a biya su ku?in ratsawa ta sararin samaniyarsu.

To maimakon ku?in da za a biya na ?asa ?aya, wato Sudan. (A yanzu) Mai yiwuwa a biya na ?asashe da yawa. Kun ga an samu ?arin ku?a?e kenan,” Abdullahi Har?awa ya tabbatar.

Na biyu, a cewarsa, tun da akwai ?arin tazara kamar na sa’a biyu a tafiyar jirgin sama, man da jirgin yake sha ma zai ?aru kenan, lamarin da shi ma ke nufin ?arin ku?i game da batun jigilar alhazai.

Abdullahi Har?awa ya ce kamfanonin sufurin jiragen sama sun sa hannu a kan yarjejeniyar jigilar aikin hajjin na bana ne bayan an daddale tsakaninsu da Hukumar kula da Aikin Hajji ta ?asa kan matsalolin da za a iya fuskanta.

Ya ce: “Sun amince sun sa hannu ?in, amma an yarda akwai bukatar a san yadda za a yi, a ?ara musu farashi”.

Jami’in na hukumar aikin hajjin Najeriya ya ce sai dai shi maniyyaci ya riga ya biya ku?i, “bisa yadda aka tallatar masa.

Don haka ba a cimma wannan matsayar ba tukunna”.

An tambayi Abdullahi Magaji Har?awa ko hakan na nufin mai yiwuwa ko za a bu?aci maniyyaci ya biya ?arin ku?i? Sai dai ya ce zuwa yanzu, ba zai iya tabbatar da hakan ba.

“Amma dai abin da nake tabbatar miki shi ne, eh akwai bukatar ?arin ku?i. Akwai tazara da yawa. Akwai ?awainiya da yawa. ?arin ku?in nan daga ina zai fito? Shi ne ba a cimma matsaya ba”.

Kamfanonin sufurin jiragen saman da suka sa hannu kan yarjejeniyar sun ha?ar da – Air Peace da Azman Air Services da Aero Contractor da kuma Max Air.

Exit mobile version