Site icon Muryar 'Yanci

Hajjin Bana: Alhazzai Za Su Biya Kudin Kujera Miliyan Biyu Da Rabi

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar, hukumar Aikin Hajji ta ?asa (NAHCON) Ta fitar da farashin ku?in kujerar aikin hajji.

Hukumar ta bayyana cewar masu son zuwa aikin Hajji na shekarar 2022 a Saudiyya za su biya kusan naira miliyan biyu da rabi ku?in kujera a hajjin bana.

A cewar hukumar, mazauna yankin arewacin Najeriya za su biya jumillar ku?i naira 2,449,607.89, yayin da na yankin kudu za su biya 2,496,815.29.

Mazauna jihohin Borno da Yola kuma za su biya 2,408,197.89, a cewar hukumar.

Exit mobile version