Site icon Muryar 'Yanci

Hada Taura Biyu A Baki: PDP Ta Nemi Kotu Ta Tsige Mai Mala Daga Gwamna

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar PDP ta fara daukar matakin doka na tsige gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni daga mukaminsa bisa zargin sabawa kundin tsarin mulki da ya hana shugaba gudanar da ofisoshi biyu a lokaci daya.

Jam’iyyar PDP a cikin karar da aka shigar ranar 12 ga watan Agusta, tana zargin Buni ya sabawa sashi na 183 na kundin tsarin mulki saboda a matsayin gwamna ya yarda ya zama Shugaban Kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC.

Wadanda suka shigar da karar sun hada da Umar Damagum da Baba Aji ta hanyar Emeka Etiaba (SAN), sun dage cewa Buni ya zama ba gwamna ba daga lokacin da ya yarda ya karbi matsayin Shugaban Kwamitin rikon kwarya na APC.

Don haka masu shigar da karar sun nemi kotun da ta umarci babban alkalin jihar Yobe ko wani babban mutum da ke kusa da babban alkalin da ya gaggauta rantsar da Damagum da Aji a matsayin Gwamna da Mataimakin Gwamnan Jihar Yobe.

PDP ta bayyana haka ne saboda Damagum da Aji su ne ‘yan takarar jam’iyyar PDP wadanda suka zo na biyu a zaben gwamna na 2019.

Exit mobile version