Site icon Muryar 'Yanci

Gwamnoni Za Su Yi Farin ?ango Zuwa APC Kwanan Nan – Ganduje

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar mai girma Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa jam’iyya mai mulki ta APC ta fara shirye-shiryen kar?ar wasu gwamnonin PDP a dai-dai lokacin da za?en 2023 ke ?aratowa.

Idan zaku iya tunawa a baya-bayan nan mun kawo muku rahoton sauya she?ar gwamnan Jihar Cross Rivers, Ben Ayade, daga PDP zuwa APC. Yayin da a kwanan nan ake ta ra?e-ra?in gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ka iya komawa APC a ko wane lokaci.

Ganduje ya fa?i haka ne yayin da kwamitin rijista na APC ya kai masa ziyara a gidan gwamnatin Kano dake Abuja, wanda Farouk Adamu Aliyu, yake jagoranta.

Gwamnan yace: “Ina mai sanar daku cewa akwai alamun wasu gwamnoni zasu dawo jam’iyyar mu ta APC daga wasu jam’iyyu. Jam’iyyar mu na ?ara ?arfi a kullum.”

Ganduje ya musanta zargin cewa an yiwa wasu mambobin APC magu?i yayin gudanar da rijista da kuma sabunta rijistar a jihar Kano, inda aka jiyo shi yana cewa: “Babu wanda aka yiwa magu?i a lokacin, amma duk wanda ke ganin an mishi magu?i kofar mu a bu?e take, a shirye muke mu yiwa kowa rijista, ba ruwanmu da ra’ayinsa game da APC.”

Exit mobile version